Winamp Logo
Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle Cover
Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle Profile

Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle

Hausa, Social, 1 season, 118 episodes, 19 hours, 20 minutes
About
Muna gabatar muku da shirye-shirye masu ƙayatarwa da suka shafi al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi da mabiya addinai daban-daban da nufin kyautata tsarin zamantakewa da fahimtar juna ta hanyar tuntuɓar juna da shawarwari tsakani ba tare da nuna fifiko akan wani ba.
Episode Artwork

Taba Ka Lashe 18.07.2024

Shirin ya duba busa algaita da ake yi a lokacin taron sarakuna ko biki ko wata haduwa a tsakanin Barebari ko Kanuri .
7/18/20249 minutes, 57 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 10.07.2024

Wani wuri a Zuru da ke jahar Kebbi ana kiransa da suna (Girmace), a wannan wuri ne da mutane ke rayuwa tare da Kadoji.
7/16/20249 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 03.07.2024

Masarautun gargajiya na zama tushen shugabanci da jagorancin al'ummar arewacin Najeriya, wanda ko a zamanin Turawan mulkin mallaka an ga yadda suka tafi tare da su. Sarakuna kan zamo alkiblar al'umma ta fuskar gudanar da rayuwa da dukkan al'amura na yau da kullum, kama daga harkokin neman ilimi da kasuwanci da zamantakewa da sana'o'i da dukkan lamuran da suka shafi al'adu da ma addinai.
7/9/202410 minutes, 3 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 26.06.2024

Akwai lokacin da 'yan bori da matsafa ke haduwa a sassan yammacin Jamhuriyar Nijar.
7/2/202410 minutes, 1 second
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 12.06.2024

Sana’ar Wanzanci da a baya ta shahara musamman yankin Arewacin Najeriya yanzu ta fara gushewa saboda yadda masu aski na zamani su fito su ka mamaye sana’ar tsakanin Hausawa.
6/18/20249 minutes, 40 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 22.05.2024

Rubutun Hausa
5/28/20249 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 15.05.2024

Shiri ne kan yadda kabilar Gwari ko Gbagi ke daukar kaya a kafada maimakon kai.
5/21/20249 minutes, 27 seconds
Episode Artwork

Taba ka Lashe 01.05.2024

Shirin ya duba al'adar wasa tsakanin abokan wasa na jini wato dan mace da dan namiji da sauran wasanni da ke tsakanin hausawa da sauran kabilu.
5/1/20249 minutes, 38 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 17.04.2024

4/23/20249 minutes, 42 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 10.4.2024

Shirin Taba Ka Lshe game da kabilun da suka shiga kurmi daga sassan Najeriya da yarda suke samun cin karo da na kabilar Yarabawa.
4/16/20249 minutes, 34 seconds
Episode Artwork

Taba ka Lashe 21.03.2024

Shirin ya duba yadda Bahaushe da masu mulkin mallaka suka sauya wa yankuna ya yi tasiri a bunkasar al'adun matunen yankunan da abin ya shafa a Kamaru.
3/21/20249 minutes, 54 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 14.02.2024

Bikin taushen fage da dubban al’ummar garin Tsangaya da ke karamar hukumar Albasu a jihar Kano da ke Najeriya
2/27/20249 minutes, 42 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 21.02.2024

Al'ummar Jamhuriyar Nijar na ci gaba da jimamin rasuwar Alhaji Mahaman Kanta fitaccen dan Jarida kuma wakilin Deutsche Welle na farko a Jamhuriyar Nijar.
2/27/202410 minutes, 25 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 07.02.2024

Ko kun san Kabilar Sayawa a jihar Bauchi da ke Najeriya, na da irin nata tsarin yadda take gudanar da bikin aure? Shirin Taba Ka Lashe
2/13/20249 minutes, 36 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 03.01.2024

Shirin ya duba gasar karatun alkurani da aka shirya a jihar Yobe domin zabo gwarzaye da za su wakilci Najeriya a gasar duniya da ake yi, inda aka samu manyan baki da Sarkin Musulmin Najeriya.
1/3/20249 minutes, 37 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 27.12.2023

Shirin ya duba bikin Hausa Kirista da aka saba gudanarwa a duk ranar 26 ga watan disambar kowace shekara sakamakon kirisimeti. Za mu ji yadda bikin ya samo asali a cikin bukukuwan al'adun Hausawa da ma yadda aka gudanar da shi.
12/27/20239 minutes, 42 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 20.12.2023

12/26/20239 minutes, 48 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 15.11.2023

Shin kun san tarihin Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja mazan fama a shirin harkokin wasan kwaikwayo a arewacin Najeriya?
11/21/20239 minutes, 56 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 08.11.2023

Ko kun san cewa marigayi Shehu Usman dan Fodiyo ya rubuta tarin litattafan ilimi, shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari a kai.
11/13/20239 minutes, 52 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 25.10.2023

Kabilar Dagomba guda ce daga cikin kabilun da ke da matukar tasiri a arewacin Ghana kuma ta yi biki nadi a birnin Kolon na Jamus.
10/31/20239 minutes, 52 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 11.10.2023

10/17/20239 minutes, 39 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 04.10.2023

Yadda al'umma a yankin Hausawa suke fadin sunayen yaransu na farko sabanin yadda aka sani a baya.
10/10/20239 minutes, 56 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe:26.09.2023

Shirin ya duba muhimmancin tagwaye a lokacin aure a jihar Gaya ta Jamhuriyar Nijar, inda ake gayyatar 'yan biyu da ke a cikin gari da kewaye domin kawo gudurmuwa a wajen bikin 'yan biyu.
9/26/20239 minutes, 4 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe:19.09.2023

Shirin ya nufi masarautar Abzinawa ta yankin Zinder da ke Jamhuriyar Nijar don duba tarihi da kuma al'adun masarautar har ma da irin rawar da take takawa wajen sasanta rikice-rikice tsakanin al'umma.
9/19/20239 minutes, 51 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: (06.09.2023)

Shirin na wannan lokaci, ya halarci bikin nunin fasahar zane-zane da fenti da rubuce-rubucen ayoyi ko surori da alamomi na tsayuwa ko wakafi ko kuma kowasula irinsa na farko da makarantar al-Kur'ani da take koyar da wannan darasi ta shirya a Kano.
9/12/20239 minutes, 46 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 24.08.2023

Shirin ya duba yadda Mata 'yan kabilar Kanuri ke ci gaba da rike al'adar nan ta cire takalmansu domin girmama maza
8/29/20239 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 02.08.2023

Shirin ya yi nazari kan yadda ske yin watsi da al'adun Hausawa na iyayen da kakanni a yayin bikin aure a Najeriya.
8/8/202310 minutes, 3 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: Al'adun Igbo

'Yan kabilan Igbo sun kasance a yankin kudu maso gabashin Najeriya kuma suna al'adu masu yawa.
7/25/20239 minutes, 48 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe

Jihar Tahoua da ke Jamhuriyar Nijar ta yi rashin wata fittaciyar mawakiya.
7/18/20239 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe 27.06.2023

Shirin ya duba yadda zumunci ya samu koma baya a kasar Hausa sabanin shekarun da suka gabata ba. A wancan lokaci, rike zumunci ya haifar da zaman lafiya da so da kauna da fahimtar juna da tausayin juna. Amma yanzu an iso wata gaba da al'amarin ya lalace. Me ya haifar da hakan? Ina mafita?
6/27/20239 minutes, 32 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 31.05.2023

Shin ko kuna da masaniya kan wata al'ada da ake yi wa lakabi da "Tarkama"? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan wannan al'ada.
6/6/202329 minutes, 48 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 17.05.2023

Shirin ya yi nazari kan wasu daga cikin al'adun Tubawa.
5/23/20239 minutes, 56 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 10.05.2023

Masarautar Kano ta nada sabbin hakimai a kokarinta na kyautata al'ada da riko da tsarin da magabata suka dora ta a kai. Ko ya ya ake nadin sarautar hakimci a kano? Ko ya ya masarautun arewacin Najeriya ke aron sarauta a tsakaninsu.?
5/16/20239 minutes, 32 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 03.05.2023

Shirin ya yi nazari kan yadda ake gudanar da bukukuwa da ma hawan salla a jihar Katsina da ke Najeriya
5/9/20239 minutes, 41 seconds
Episode Artwork

MMT/ Kultur(05-04-23)Niger Ramadan Tashe - MP3-Stereo

Taba Ka Lashe: Tashe lokacin Azumi
4/11/20239 minutes, 37 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe

Gidan tarihi na Kanta Museum dake garin Argugu a jihar Kebbi da ke Najeriya na kara samun karbuwa da tagomashi.
3/14/20239 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 01.03.2023

Ko kun san tabarbarewar tarbiyya da watsi da al'adu kan kawo lalacewar matasa su shiga wasu miyagin dabi'u da kuma ka iya shafar zamantakewar al'umma? Dangane da haka ma'aikatar kula da al'adu ta Jamhuriyar Nijar ta dauki matakin dakile wannan matsala. Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari kan matakan.
3/7/20239 minutes, 42 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: Wasu kabilru sun hade domin fahimtar juna

Wasu kabilu kimanin takwas a karamar hukumar Toro da ke jihar Bauchi a Najeriya sun hade wuri guda tare da dabbaka al'ada daya.
2/21/202310 minutes, 8 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 24.01.2023

Ko kun san al'adar mutanen Zuru da ke jihar Kebbin Najeriya? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari.
1/30/20239 minutes, 43 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe 17.01.2023

Yadda al'adar Fulani ta auren gida ta fara sauyawa sannu a hanakli a Najeriya.
1/24/20239 minutes, 48 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 04.01.2023

Ko kun san yadda rayuwar marigayi Fafaroma Benedikt ta kasance? Shirin Taba Ka Lashe
1/9/20239 minutes, 52 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 30.11.2022

Ko kun san yadda rayuwar 'yan kabilar Pyemawa da ke karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau a Najeriya take? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari.
12/6/202210 minutes, 4 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe

Taba Ka Lashe: Kowace shekara a jihar Agadez da ke Jamhuriyar Nijar ana wani bikin Fulani
11/15/20229 minutes, 35 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 26.10.2022

Al'adar cire guda ce daga cikin al'adun da aka san 'yan kabilar ta Fulani Boraroji da ita a yankunan da suka fi yawa na kasashen Afirka, Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan wannan al'ada.
11/1/20229 minutes, 53 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe 19.10.2022

Shirin ya duba yadda bikin Maulidi na bana ya gudana a kasashen Nijar da Najeriya.
10/25/20229 minutes, 31 seconds
Episode Artwork

Taba ka Lashe 12.10.2022

Shirin ya duba yadda zamani ya sauya tunanin al'ummar Hausawa da dama kan kyamar mahauta masu sana'ar sayar da nama da kuma auren 'ya'yansu.
10/18/20229 minutes, 47 seconds
Episode Artwork

Taba ka Lashe 15.09.2022

Saurari shirin don jin yadda miliyoyin al'umma 'yan kabilar Tubawa da suka warwatsu a kasashe da dama na Kudu da hamadar Sahara suka gudanar da bikin ranar Tubawa.
9/27/20229 minutes, 34 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 14. 09. 2022

Ko kun san abin kidan da ake kira da Kuntigi da ma su kanus makadan Kuntigin? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan kidan da makadan.
9/20/20229 minutes, 46 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 07.09.2022

Ko kun san cewa ana gudanar da babban taro da ke hada kan dukkannin majami'un addnin Kirista na fadin duniya duk shekara? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan wannan taro, musamman yadda mabiya addnin Kirista daga Najeriya da suka halarci taron suka nemi a tallafawa kasar da ke cikin halin rashin tabbas.
9/13/20229 minutes, 54 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 31.08.2022

Ko kun san akwai wasa tsakanin kaka da jika a kasar Hausa? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan wannan al'ada.
9/6/20229 minutes, 44 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: (24.08.2022)

Ko kun san wasu malaman jami'a a Katsina sun koma sana'ar gado sakamakon yajin aikin kungiyra malaman jami'o'i ta kasar ASUU? Ku biyo mu domin jin wanda ya rungumi sana'arsa ta gado wato wanzanci.
8/30/20229 minutes, 36 seconds
Episode Artwork

Taba Ka lashe: Makwabtaka

Zamani ya taho da abubuwa da dama, kuma wannan shirin ya fito da bambancin yanayin zamantakewar al'ummar Hausawa a can baya da kuma na wannan zamanin.
8/23/20229 minutes, 54 seconds
Episode Artwork

Shirin Taba Ka Lashe kan kudin shara

Shara wata al'ada ce da malam Bahaushe ya kirkira tare da dangantawa da lokacin kololuwa na ibada bayan da ya karbi addinin Muslunci.
8/9/20229 minutes, 38 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 06.07.2022

Shirin ya yi nazari kan kidan kalangu, ku biyo mu domin ku rausaya.
7/12/20229 minutes, 51 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: Sauye–sauyen zamani ga al’adar aure a kasar Hausa

Shirin Taba Ka Lashe kan sauye–sauyen zamani ga al’adar aure a kasar Hausa
6/21/20229 minutes, 48 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 08.06.2022

Shirin ya yi nazari kan yadda mutane musamman a kasar Hausa, ke yin adashi domin taimakon kansu.
6/14/20229 minutes, 33 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe (25+26.05.2022)

Kungiyar DRPC na daga cikin kungiyoyi a jihar Jigawa da ke fadi-tashi wajen ganin sun ciyar da fannin ilimi gaba a Najeriya.
5/31/20229 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe (18.05.2022)

Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya garzaya jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijar, inda ya yi nazari kan al'adar maita.
5/24/20229 minutes, 35 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: Sallah a masarautar Abzin

Saurari yadda aka gudanar da bikin Sallah karama a fadar sarkin Abzin na jihar Agadez. An shafe kwanaki uku ana bukukuwan al’adar da ke kayatar da jama’a.
5/10/20229 minutes, 32 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: Batun amfani da harshen gida a Jamhuriyar Nijar

Shirin ya yada zango a birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar inda muka duba batun yadda iyaye ke sakaci wajen koyar da yara harshen gida.
5/3/20229 minutes, 52 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lahe: 23.03.2022

Ko Kun san yadda al'adar tauri take, a Jamhuriyar Nijar musamman a birnin Damagaram? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari.
3/29/20229 minutes, 39 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe 16.03.2022

Al'adar bikin aure a kasar Guddirawa da ke jihar Bauchin Najeriya mai dumbin tarihi.
3/22/20229 minutes, 54 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: Al'adar bikin aure a Guddiri

Aure na daya daga cikin al'adun da Guddurawa suke masa hidima ta gani a fada fiye da duk wata al'adar su, kama daga farkon nema tsakanin saurayi da budurwa har zuwa lokacin bayarwa da mai gaba daya lokacin bikin auren. Kuma har zuwa yanzu guddurawa ba su bari ba. Wannan shi ne batun a shrin Taba Ka ashe na wannan mako ya yi duba a kai. Daga kasa za a iya sauraon sauti
3/15/20229 minutes, 54 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: Al'adar bikin aure a Guddiri

Al'adar bikin aure a Guddiri a Jihar Bauchi dadaddiyar masarauta ce mai dumbin tarihi, kuma guddurawa suna da wasu fitattun al'adunsu da suka banbanta su da sauran masarautun Bauchi.
3/15/20229 minutes, 54 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 02.03.2022

Ko har yanzu ana amfani da wakokin gargajiya da kayan kidan harshen Hausa a kasar Hausa? Shirin Taba Ka Lashe.
3/8/20229 minutes, 36 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: Rayuwar Musulmi da Kirista

Musulmi da Kirista a Jihar Filaton Najeriya na zaune a unguwani dabam-dabam sabanin yadda a baya al'ummomin biyu ke zaune wuri guda suna cudanya.
2/15/20229 minutes, 53 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe 02.01.2022

Shirin na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan kirari. Ya al'adar kirari take a kasashen Afirka?
2/8/20229 minutes, 56 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 26.01.2022

Shirin na wannan lokaci ya ziyarci jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, inda ya gano wani Masallaci da ya kwashe shekaru aru-aru.
2/1/20229 minutes, 46 seconds
Episode Artwork

Jamhuriyar Nijar: Tarihin addinin Kirista

Tarihin addinin Kirista a Jamhuriyar Nijar a tsawon shekarun da suka gabata.
1/18/202210 minutes, 7 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: Nazari kan sabon salo na yin amfani da kafafen sadarwar zamani da mawakan Jamhuriyar Nijar ke yi

Nazari kan sabon salo na yin amfani da kafafen sadarwar zamani da mawakan Jamhuriyar Nijar ke yi wajen tallatawa ko sayar da wakokinsu
1/11/20229 minutes, 50 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 29.12.2021

Ko kun san su wanene mafarauta da 'yan tauri da kuma yadda suke samun taurin? Ku saurari Shirin Taba Ka Lashe.
1/4/20229 minutes, 30 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 22.12.2021

Shirin ya duba yunkurin farfardo da wata sarautar gargajiya ta kabilar Abzinawa a garin Afess na jahar Agadez a Nijar.
12/28/202110 minutes, 8 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 15.12.2021

An gudanar da bikin nadin sababbin sarautu, a masarautar Hausawan Turai. Karin bayani cikin Taba Ka Lashe.
12/21/20219 minutes, 41 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 08.11.2021

Mata na taka muhimmiyar rawa, wajen magance rikice-rikicen kabilanci da na addinai da makamantansu. Shirin Taba Ka Lashe.
12/14/20219 minutes, 47 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 24.11.2021

Ko kun san yadda mabiya darikun Sufaye ke ziyara Kushewar Waliyai a Maroko? Shirin Taba Ka Lashe.
11/30/20219 minutes, 43 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe

Wurin da ake tsugune da daruruwan mata da ake zargi da aikata maita a wata cibiya ta musamman da ake wa lakabi da "Sansanin mayu” a arewacin Ghana.
11/16/20219 minutes, 43 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 27.10.2021

A duk ranakun 12 ga watan Rabi'ul Auwal na ko wacce shekara, al'ummar Musulmi a fadin duniya kan yi bukukuwan tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAAW). A wannan shirin mun yi nazarin yadda aka gudanar da bukukuwan na bana a jihar Kano da ke Najeriya.
11/2/20219 minutes, 52 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 06.10.2021

Al'adar Cire tsakanin Fulani Bararoji inda ake cirén mace a duk lokacin bukin makiyaya kamar Cure Salé ko Bukin Lasar Gishiri, inda zarumi kafin rufe bukin kan yi amfani da asiri don ciren macen da ta burge shi ko da kuwa tana da aure. Sai dai wannan al'ada ta fara bacewa saboda shigowar addini.
10/13/20219 minutes, 37 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe 22.09.2021

Yadda zamani ke shirin gusar da al'adun gargajiyan jahar Gaya a jamhuriyar Nijar. Latsa kasa don jin cikakken shirin.
9/28/20219 minutes, 44 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 15.09.2021

Amfani da ahnnun hagu, halitta ce da daga Allah. Sai dai wasu na fuskantar kalubale sakamkon wasu al'adu da ma addinai. Ku saurari shirinmu na Taba Ka Lashe.
9/21/202110 minutes, 37 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 01.09.2021

Ko kun san yadda kabilar Igbo da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, ke bikin binne gawa? Shirin Taba Ka Lashe.
9/7/20219 minutes, 32 seconds
Episode Artwork

Taba ka lashe 04.05.21

Al'adar wasan kara a yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar wanda matasa ke yi a lokacin kaka bayan girbin amfani gona
8/31/20219 minutes, 50 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 11.08.21

Ko kun san cewa akwai fadar Hauasawa har ma da sarkinsu a Turai? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan batun wannan sarauta.
8/24/202110 minutes, 21 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 04.08.2021

Ko kuna da masaniya kan yadda al'adar wasan kara ke gudana a jihar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar? Shirin Taba Ka Lashe
8/10/20219 minutes, 50 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 21.07.2021

Shadi, dadaddiyar al'ada ce ta Fulani da aka fi amfani da ita wajen neman aure. Sai dai a yanzu al'amura sun sauya. Ko ya al'adar ta shadi take gudana a yanzu? Shirin Taba Ka Lashe.
7/27/20219 minutes, 30 seconds
Episode Artwork

Taba ka Lashe 21.07.2021

Al'adar Sharo na fulani wata dadaddiyyar al'ada ce mai muhimmanci ga fulani wacce tun shekaru masu yawa suke yin ta musamman domin hada aure tsakanin samari da yan mata.
7/20/20219 minutes, 30 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 07.07.2021

Ko kun san irin baiwar da aka yi ittifakin cewa 'yan tagwaye ko kuma 'yan biyu na da su a kasashen Hausa masu tarin al'adu? Shirin Taba Ka Lashe.
7/13/20219 minutes, 42 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 30.o6.2021

Jamhuriyar Nijar na fuskantar tarin matsaloli a fannin shirya fina-finai, sai dai tuni aka dauki mataki domin shawo kan wadannan matsaloli.
7/6/20219 minutes, 50 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 23.06.2021

Shirin na wannan lokaci, ya yi nazari ne kan taron 'yan jaridu na duniya da tashar DW ta saba shiryawa duk shekara, wato Global Media Forum.
6/29/20219 minutes, 44 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 16.06.2021

Bikin nadin fadawan masarautar Tsibiri, cikin gundumar Dogon Doutchi da ke Jamhuriyar Nijar. Shin ya bikin ke gudana? Shirin Taba Ka Lashe.
6/22/20219 minutes, 32 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 19.05.2021

Al'adar hawan kaho a Jamhuriyar Nijar, dadaddiyar al'ada ce ta ake gudanar wa a karshen watan azumin Ramadana na kowacce shekara. Ku biyo mu domin jin yadda al'adar take.
5/25/20219 minutes, 50 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe 14.04.2021

Dinke baraka bayan cika shekaru 30 da aukuwar wani rikici mai nasaba da kabilanci a jihar Bauchi da ke Najeriya wanda ya salwantar da rayukan jama'a masu tarin yawa.
4/20/20219 minutes, 39 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: Zamantakewar Yarbawa da Hausawa

Shirin yayi nazari kan zamantakewar Fulani da Hausawa tun bayan fuskantar barazana ta asarar rayuka da dukiya a wasu jihohin kudu maso yammacin Najeriya.
4/13/20219 minutes, 44 seconds
Episode Artwork

Shirin Taba Ka Lashe 24.03.2021

Kalubalen da iyaye 'yan asalin kasashen nahiyar Afirka dama yaran da suka haifa a kasar Amirka suke fuskanta a yayin da aka ce yaran sun kai minzanin yin aure.
3/30/20219 minutes, 53 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 17.03.2021

Ko kun san cewa a Najeriya akwai wani kogi da ke da ruwan sanyi da kuma tafasasshen ruwa a cikinsa? Ku biyo mu garin Tingno da ke jihar Adamawa.
3/23/20219 minutes, 33 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe 17.02.2021

Wasan kwaikwayo tamkar madubi ne na rayuwa da zamantakewar al'umma a raya al'adun gargajiya da zamantakewar bahaushe a kasar Hausa musamman a tarayyar Najeriya.
2/23/20219 minutes, 39 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 10.02.2021

Sarakunan gargajiya da kungiyoyin manoma da makiyaya a Jamhuriyar Nijar, na fadakar da mutane kan muhimmancin zaman lafiya domin kaucewa rigingimu duba da irin abubuwan da suke faruwa a Tarayyar Najeriya da sauran kasashe da ke makwabtaka da Nijar din.
2/16/20219 minutes, 34 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 03.02.2021

Kabilar Yandang wata kabila ce da ke karamar hukumar Mayo-Blewa a jihar Adamawan Tarayyar Najeriya. Shirin Taba Ka Lashe ya leka domin kawo muku yadda annobar corona ta shafi yadda suke gudanar da bukukuwansu na al’ada a wannan shekarar.
2/9/20219 minutes, 30 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 13.01.2021

Ko kun san hanyoyin da za a bi wajen hada kan mabiya mabanbamtan addinai a Najeriya? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan wannan batu.
1/19/20219 minutes, 46 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 23.12.2020

A birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar, hadakar kungiyoyin addinai sun bayar da horo ga sarakunan gargajiya da malamai da kuma mata dangane da kyautata zamantakewa a tsakanin al'umma domin a samun zaman lafiya. Ku saurari shirin Taba Ka Lashe.
1/5/20219 minutes, 40 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 30.12.2020

Yadda aka gudanar da bukukuwan Kirsimeti a kasar Ostireliya, a adaidai lokacin da duniya ke fama da bala'in annobar coronavirus.
12/28/20209 minutes, 39 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: Al'adun auren Abzinawa

Agadez tana daya daga cikin jihohin Jamhuriyar Nijar duba yada al’ada auren Abzinawa.
11/24/20209 minutes, 51 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 14.10.2020

Shirin ya yi nazari kan masarautar Zazzau da ke garin Zariya a jihar Kadunan Najeriya. Masarautar ta Zazzau dai na daga cikin masarautu masu dimbin tarihi a kasar Hausa.
10/20/20209 minutes, 24 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 30.9.2020

Ko kun san cewa a wani gari da ke jihar Katsina a Tarayyar Najeriya, akwai al'ummar Musulmi da Kirista da ke zaune kusan shekaru 100 ba tare da an taba jin kansu ba? Ku biyo mu domin jin dalili.
10/6/20209 minutes, 48 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 16.09.2020

Shin ko kun san cewa har yanzu a yankin arewacin Najeriya akwai masarautar da ke karkashin mulkin mace? Ku biyo mu zuwa jihar Adamawa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar.
9/22/20209 minutes, 24 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe 09.09.2020

Bikin al'adun gargajiya na Biano da akan gudanar kowace shekara a birnin Agadez na jamhuriyar Nijar a wannan shekarar ta 2020 ya zo a daidai lokacin da ake fama da annobar Korona ko Covid 19. Amma duk da haka shugabanni a wajen bikin sun jaddada bukatar raya al'adar ta gargajiya.
9/15/20209 minutes, 40 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 02.09.2020

Shirin zai leka Tarayyar Najeriya, inda zai yi nazarin wani abu guda da ya hada manyan kabilun kasar wato Hausawa da Igbo da kuma Yarabawa, wannan abu kuwa shi ne: "Goro."
9/8/20209 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 26.08.2020

San'ar wanzanci dadaddiyar sana'a ce a kasar Hausa, shin wanne irin tasiri sana'ar ta wanzanci ke da shi ga al'adun Hausawa? Shirin Taba Ka Lashe.
9/1/20209 minutes, 42 seconds
Episode Artwork

Taka Ka Lashe: 12.08.2020

A cikin shirin za a ji cewar a karon farko a tarihi wani mawakin Abzinawa na kasar Nijar mai suna Alhousseini Mohamed Anivolla da kuma wani takwaransa mawaki kuma Injiniyan hada sauti na kasar Habasha mai suna Gurum Masama sun fidda faifan wakoki na hadin gwiwa da ya kunshi wakoki masu armashi.
8/18/20209 minutes, 57 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 05.08.2020

Al'ummar Gbagyi na zaman guda daga cikin kabilun da ke yankin Arewa maso Tsakiyar Najeriya. Ko wanne suna aka fi sanin wanna lkabila da shi?
8/10/20209 minutes, 36 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 29..07.2020

A ranar Jumma'ar da ta gabata ne, alumar Musulmi a fadin duniya suka fara shagulgulan babbar Salla ko kuma Sallar layya. To sai dai a bana bikin ya zo ne daidai lokacin da duniya ke ci gaba da fama da annobar corona da ta janyo koma baya a bangarori dabam-dabam na rayuwa.
8/4/20209 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 22..07.2020

Annobar cornavirus da ta addabi duniya, ta yi mummunan tasiri ga al'amura da dama ciki kuwa har a al'adu. Shun ko ya annobar ta shafi makada da mawakan gargajiya? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari a kai.
7/28/20209 minutes, 35 seconds
Episode Artwork

Wariyar launin fata ga bakar fata a Maroko

An hana yin magana game da wariyar launin fata a Maroko. An kuma boye batun bakar fatan kasar dalilin haka ya sa ba a iya magana game da irin matsalolinsu na wariya wannan shi ne batun da shirin Taba Ka Lashe ya duba.
7/21/20209 minutes, 44 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 08.07.2020

Wanne irin abincin gargajiya na kasar Hausa kuka sani? Ya aka yi abincin gargajiya ke bacewa sannu a hankali a kasar Hausa? Ku biyo mu cikin Shirin Taba Ka Lashe.
7/14/20209 minutes, 3 seconds
Episode Artwork

Nijar: Matsafa da al'adun gargajiya

A Jamhuriyar Nijar har yanzu matsafa magadan gargajiya na rike da wata al'adar da ake kira ''Tarkama'' da ke tattare da mamaki da ke zakulo masu aikata barna daga cikin al'umma, batun da shirin Taba Ka Lashe ya duba.
7/7/20200
Episode Artwork

Sauraro da kallo na barazana ga Hausa

Al'adar karance-karance ta ja baya a wannan zamanin musamman ma a tsakanin Hausawa ta la'akari da yadda mafi akasarin jama'a suka fi karkata zuwa ga kallo da sauraro. Wannan shi ne batun da shirin Taba ka Lashe ya duba.
6/30/20209 minutes, 27 seconds
Episode Artwork

Wasan watan bakwai don rokon damina mai albarka

A Jamhuriyar Nijar a ko wace shekara a wannan lokaci na shigar damina ana gudanar da wasan watan bakwai domin samun saukar damina mai albarka da kuma rokon aljannun ruwa kar a samu ambaliyar ruwa da barna ko asarar rai sakamakon saukar ruwa mai yawa.
6/23/20209 minutes, 44 seconds
Episode Artwork

Taba Ka Lashe: 10.06.2020

Ko kun san yadda zamantakewa take a tsakanin kabilun da ke rayuwa a jihar Bornon Najeriya? Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi mana nazari.
6/16/20209 minutes, 45 seconds