Winamp Logo
Mu Zagaya Duniya Cover
Mu Zagaya Duniya Profile

Mu Zagaya Duniya

Hausa, Political, 1 season, 75 episodes, 1 day, 55 minutes
About
Wannan Sabon Shiri ne da ke tattauna Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya. Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.
Episode Artwork

Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Sarki Muhammadu Sunusi kan mukaminsa

Gwamnan Kano Abba Yusuf ya rattaba hannu a wata doka  mai rusa ga baki daya masarautun Kano inda ya mayar da Sarki Muhammadu Sunusi kan mukaminsa.Bashir Ibrahim Idris dangane da wannan mataki ya tattauna da Abdoulkarim Ibrahim da Nura Ado Suleiman a cikin shirin Duniyar mu a yau daga nan sashen hausa na Rfi.
5/25/202420 minutes, 29 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Bikin cika shekaru 17 da kafuwar Sashin Hausa na RFI

Daga cikin labarun da shirin na Muzagaya Duniya ya sake waiwaya akwai cikar Sashin Hausa na RFI shekaru 17 cif da kafuwa. Sai kuma matakin rushe sabbin masarautun da ya baiwa gwmna Abba Kabir Yusuf damar sake naɗa Sarki Muhammadu Sunusi na II a matsayin Sarkin Kano na 16. A Guinea kuwa, gwamnatin sojin da ke jagorantar ƙasar ce ta rufe wasu kafafen yaɗa labarai da suka hada da gidan talabijin da kuma gidajen radio da dama.Kotun Duniya ta baiwa Isra’ila Umarnin Dakatar da hare-haren da ta kaiwa a Rafah.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.....
5/25/202420 minutes, 21 seconds
Episode Artwork

Tattaunawa da Dr Kasim Garba Kurfi a shirin Duniyarmu a yau

Wannan shiri na Duniyarmu a yau zai dinga muhawara kan harkokin yau da  kullum da ke dauke hankalin jama'a a duk ranar Asabar daga karfe 5.Shirin na wannan mako ya karbi bakucin Dr Kasim Garba Kurfi mai sharhi kuma masanin tattalin arziki.
5/19/202420 minutes, 29 seconds
Episode Artwork

Mutane 15 ne suka rasa mutu sanadiyar harin da matashi ya kai Masallaci a Kano

Daga cikin labarun da shirin wannan makon ya ƙunsa akwai harin da wani matashi a Kano ya kaiwa Masallaci ta hanyar cinna masa wuta, wadda zuwa lokacin gabatar da wannan shiri aka tabbatar da salwantar rayukan mutane 15 daga cikin akalla 30 da ke cikin Masalacin. Shirin na kuma ɗauke da tattauna wa da tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo, kan tuntubar junan da jiga-jigan jam’iyyun dawa suka fara yi a Najeriya, don kafa sabon ƙawancen da zai tunkari jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.  Fira Ministan Senegal ya bayyana rashin gamsuwarsa kan wanzuwar sansanin sojojin Faransa a Ƙasar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.....
5/18/202420 minutes, 7 seconds
Episode Artwork

Shirin ya duba zaben Chadi da kuma shirin ECOWAS na kafar rundunar yaki da ta'addanci

Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman
5/11/202419 minutes, 51 seconds
Episode Artwork

Najeriya: Ƙarin albashi da gwamnati ta yi bai burge Ƙungiyar ƙwadago ba

Daga cikin batutuwan da shirin wannan lokaci ya waiwaya akwai, watsin da kungiyar kwadagon Najeriya ta yi da karin albashin ma’aikatan da gwamnatin kasar  ta yi.Sai kuma matakin Burkina faso na rufe karin kafafen yada labarai bisa rahoton da suka bayar na kisan fararen hula sama da 200 da sojoji suka yi.A Kenya kuwa Ambaliyar ruwan ce ta lakume rayukan mutane da dama gami da raba wasu kusan dubu 200 da muhallansu.
5/4/202419 minutes, 59 seconds
Episode Artwork

Hukumar EFCC na neman tsohon gwamnan jihar Kogi Yahya Bello ruwa a jallo

Daga cikin labarun da shirin karshen makon ya waiwaya akwai neman tsohon gwamnan jihar Kogi yahya Bello da hukumar EFCC ke yi ruwa a jallo, lamarin da ya kai ga daukar matakin dakile duk wani yunkurinsa na ficewa daga Najeriya Shirin ya kuma leƙa gabas ta tsakiya inda Iran ta ƙi fusata kan makamai masu linzamin da na’urorin tsaron sararin samaniyarta suka kakkaɓo a birnin Isfahan, waɗanda wasu majiyoyi suka ce Isra’ila ce ta yi yunkurin kai mata hari da su.
4/20/202420 minutes, 5 seconds
Episode Artwork

Muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata

Masu sauraro daga sashin Hausa na RFI cikin shirin Mu Zagaya Duniya da saba zabo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata, domin bitarsu.A ranar Larabar da ta gabata al'ummar Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da Sallar Idi Karama, wadda aka saba gudanarwa bayan kammala azumin watan Ramadan.
4/13/202420 minutes, 1 second
Episode Artwork

Karin kudin wutar lantarki ya fusata 'yan Najeriya

Shirin Mu zagaya duniya na wannan mako ya duba batun karin kudin wutar lantarki a Najeriya, halin da ake ciki a Gabas ta tsakiya da kuma rikicin siyasar Togo. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman
4/6/202419 minutes, 40 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Yadda aka ceto daliban Kuriga a Kadunan Najeriya

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Rukayya Abba Kabara ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali a makon da ya wuce ciki har da labarin yadda gwamnatin Najeriya ta ceto daliban Kuriga da ke Jihar Kaduna tare da sada su da iyalan su. Akwai dambarwar da ta zagaye batun karin kudin aikin hajji da ya gigita maniyyatan Najeriyar, sai dai kuma gwamnati ta kawo dauki a wasu jihohin.Zakuji yadda harin ta’addanci mafi muni a Rasha ya hallaka mutane sama da 130, kuma tuni wadanda aka kama suka amsa laifin su.
3/30/202419 minutes, 30 seconds
Episode Artwork

Dubi akan matakin gwamnatin mulkin sojin Nijar na katse huldar aiki da dakarun Amurka

Daga cikin muhimman batutuwan da shirin ya waiwaya a wannan makon akwai matakin Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar na kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasar da Amurka. A Najeriya kuwa hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar ce ta kawo karshen binciken da take gudanarwa kan zargin da ake yi wa rundunar sojin kasar na tilasta wa mata akalla dubu 10 zubar da juna biyun da suka samu a bisa tilas daga mayakan Boko haram
3/23/202419 minutes, 13 seconds
Episode Artwork

Matakin Najeriya na bude iyakokin da ta rufe tsakaninta da Jamhutiyar Nijar

Daga cikin labarun da shirin ya kunsa a wannan makon, akwai matakin da Najeriya ta dauka na bude iyakokin da ta rufe tsakaninta da Jamhutiyar Nijar, tare da janye baki dayan takunkuman da ta kakaba mata.Gwamnatin Birtaniya ta ce a shirye take ta baiwa ‘yan dubban ‘yan Rwanda da ke neman mafaka fam dubu uku kowannensu, to amma fa a bisa sharadin za su amince a mayar da su gida daga kasar ta Birtaniya
3/16/202419 minutes, 19 seconds
Episode Artwork

Wasu daga cikin muhimman labarun da suka wakana a makon da ya gabata

Za a ji yadda aka sake zabar sabuwar ranar gudanar da zaben shugabancin kasar Senegal,Al’ummar Sudan ta Kudu sun tsallake rijiya da baya, domin kuwa aniyar wani sabon mugu da ya bayyana ce ta watse bayanda ya yi kokarin shirya juyin mulki a kasar, duk da cewar har yanzu basu gama murmurewa daga  kazamin yakin basasar da ya tagayyara su ba, wato dai ana kukan targade karaya kuma na neman kunno kai. 
3/9/202420 minutes, 2 seconds
Episode Artwork

Wasu daga cikin muhiman labaren mako daga Rfi- Rikicin jihar Kano

Al’ummar Jihar Kano dake Najeriya sun tashi da labarin murabus din da shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi daga mukamin sa, sakamakon abinda ya kira sanyaya masa gwuiwar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, wajen sukar yadda suke gudanar da aikin su.Wannan murabus din ta haifar da mahawara mai zafi a ciki da wajen jihar Kano, tare da hudubobi a Masallatan Juma’a dangane da muhimmancin hukumar da kuma rawar da take takawa.Nasirudeen Muhammed zai jagoranci shirin.
3/2/202420 minutes, 21 seconds
Episode Artwork

Jana'izar ma'aikacin RFI Hausa, Mahammane Salissou Hamissou a garin Tsibirin Gobir

A jiya Juma'a 17 ga watan Fabrairun 2024 ne aka gudanar da jana'izar ma'aikacin RFI Hausa, Mahammane Salissou Hamissou a garin Tsibirin Gobir, Mahammane Salissou Hamissou wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Larabar da ta gabata sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.
2/17/202420 minutes, 10 seconds
Episode Artwork

Matakin hadin gwiwar da Nijar ,Mali da Burkina Faso suka dauka, na sanar da ficewa daga ECOWAS

Daga cikin muhimman labarun makon jiya da shirin ya sake waiwaya domin bitarsu akwai, matakin hadin gwiwar da Nijar da Mali da kuma Burkina Faso suka dauka, na sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS.Sai kuma sake karya darajar Naira da gwamnatin Najeriya ta yi, karo na biyu  cikin watanni 8.A Turai kuwa, za a ji yadda zanga-zangar  manoma ta bazu zuwa sassan nahiyar saboda adawa da wasu sauye-sauyen mahukuntan kasashen yankin da suka ce ba za su lamunta ba.
2/3/202419 minutes, 58 seconds
Episode Artwork

Taron Shugabannin arewacin Najeriya don lalubo hanyar magance matsalar tsaron

Masu sauraro Assalamu alaikum, Nura Ado Suleiman daga sashin Hausa na RFI ke muku maraba cikin shirin Mu Zagaya Duniya da ke waiwaye gami da zabar wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata, domin bitarsu.
1/27/202419 minutes, 56 seconds
Episode Artwork

Rikici tsakanin 'yan ta'adda a arewacin Najeriya ya illata bangaren Dogo Gide

Shirin wannan makon zai fara ne da waiwayar bata-kashin da aka yi tsakanin ‘yan bindiga a Najeriya, lamarin da ya kai ga illata bangaren daya daga cikin jagoran ‘yan ta’adddan da ya addabi jama’a.Fira Ministan Jamhuriyar Nijar ya yi tatttaki zuwa Iran, bayan ganawarsa da mahukuntan kasar Rasha inda suka karfafa yarjejeniyar tsaron da suka kullla. A gabashin Afirka kuwa cibi ne ya zama kari, domin kuwa gwamnatin sojin Sudan ce ta katse alaka da kungiyar kasashen yankin gabashin nahiyar ta Afirka, saboda gayyatar shugaba kuma Janar Abdel Fattah al-Burhan da suka yi.
1/20/202419 minutes, 49 seconds
Episode Artwork

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Abba Gida-Gida a zaben gwamnan Kano

Cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman, ya fara ne daga Kano a Najeriya, inda a ranar Juma’ar da ta gabata, kotun koli ta tabbatar da gwamna Abba Kabir Yusuf Abba na jam’iyyar NNPP a matsayin halastaccen gwamnan jihar. Shirin ya kuma sake waiwayar matakin jagoran mulkin Sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan na gindaya sharudda gabanin amincewa da shiga tattaunawa da bangaren jagoran dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo da suka shafe fiye da watanni 9 suna gwabza yaki.
1/15/202420 minutes, 1 second
Episode Artwork

Gwamnatin Najeriya ta haramta karbar shaidar karatun digiri daga Benin da Togo

Daga cikin labarun da shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya sake waiwaya a wannan makon akwai matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na haramta karbar takardun shaidar kammala karatun digiri daga jami'o'in Jamhuriyar Benin da kuma kasar Togo. Shirin ya kuma leka yankin Gabas ta Tsakiya, inda aka kashe kusan mutane 100 a wani harin ta'addanci da aka kai a kasar Iran.
1/15/202419 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

Bitar wasu muhimman labaran da suka faru a duniya cikin wannan mako

Daga cikin labarun da Shirin ya kunsa akwai batun yadda yan ta'adda a Najeriya ke gina ramu  suna boyewa, saboda barin wutar da suke sha daga sojojin kasar, sai kuma batun kammala ficewar sojojin Faransa a Nijer da dai sauran manyan labaran da suka hada da  Burkina Faso, jamhuriyar Benin, yakin Isra'ila da Hamas, tare da dokar yan ci rani da Faransa ta amince da ita.
12/23/202320 minutes, 4 seconds
Episode Artwork

ECOWAS/CEDEAO ta tabbatar da juyin mulki aka yi a Nijar

Daga cikin labarun da Shirin ya kunsa akwai matakin da kungiyar kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ko CEDAEO ta dauka na amincewa da da cewar an yi juyin Mulki a Nijar, sannan kuma ta dakatar da ita daga cikin ta har sai lokacin da sojoji suka maida wa farar hula Mulki.A Najeriya kuma, Bankin Duniya ne ya bukaci gwamnatin kasar ta fadada tsauraran matakan da take dauka na yi wa tattalin arzikin kasar garambawul, domin ceto shi daga durkushewa baki daya a nan gaba.
12/16/202320 minutes, 31 seconds
Episode Artwork

COP28 - An samar da asusun tallafa wa kasashe don yaki da matsalar sauyin yanayi

Shirin "Mu zagaya duniya" na wannan makon tare da Khamis Saleh ya waiwari babban taron sauyin yanayi na COP28 da aka faro a Dubai, inda aka samar da wani asusu na musamman da manyan kasashe za su rinka zuba kudi don taimaka kananan kasashen da matsalar da ba su suka samar ba ta fi shafa. Haka nan shirin ya kuma duba matakin da gwamnatin sojin Nijar ta dauka na dakatar da dokar hana safaran bakin haure, matakin da EU ke ganin a matsayin wata barazana ta kara yawan bakin hauren da zasu kwarara kasashenta.Ku latsa a lamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
12/2/202319 minutes, 46 seconds
Episode Artwork

Bitar wasu daga cikin labaran da suka dauki hankali na mako

Shirin zai kuma waiwayi kalaman da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yayi kan cewa Dimokaradiyar kasashen yammacin turai fa ba ta haifa wa nahiyar Afirka da mai idanu ba.  Cikin makon da ya gabata, aka shiga rudani, yayin da kuma a gefe guda aka yi ta tafka muhawara a Kano dake arewacin Najeriya, bayan da kotun daukaka kara ta fitar da takardar hukuncin da ta yanke kan shari’ar zaben gwamnan jihar a juma’ar waccan makon da ya gabata, inda ta tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe.  Sai ku biyo mu..............
11/25/202319 minutes, 50 seconds
Episode Artwork

MU zagaya Duniya: Kotun daukaka kara a Najeriya ta soke zaben gwamnan jihar Kano

Ciki Shirin wannan makon za a ji cewar Kotun Daukaka karar Najeriya ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben Kano da ya karbe kujerar Gwamnan jihar daga hannunn Abba Kabir Yusuf na NNPP ya mika ta zuwa Nasir Yusuf Gawuna na APC.Kasar Ghana ta bukaci hadin gwiwar kasashen Afirka domin tilasta wa kasashen da suka yi wa nahiyar mulkin mallaka biyansu diyya akan yadda suka azabtar da su da cinikin bayi. A Gabas ta tsakiya kuwa Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ne ya zargi mayakan Hamas da dakile duk wani yunkuri na takaita yawan rayukan fararen hular da suke salwanta a Zirin Gaza.
11/18/202319 minutes, 55 seconds
Episode Artwork

wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a wannan makon

Halin da asibitoci ke ciki a Zirin Gaza, bayan da aka shafe sama da wata guda Isra’ila na ci gaba da ruwan bama-bamai kan Falasdinawa, wadanda ya zuwa yanzu akalla dubu 40 suka jikkata baya ga sama da 10 da suka mutu a Gaza tareda Nura Ado Suleiman.
11/11/202319 minutes, 58 seconds
Episode Artwork

Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da dubu 9,000, fiye da rabinsu kuma mata ne da kananan yara

Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci a gaggauta tsagaita wuta a Zirin Gaza, tare da gargadin cewa lokaci na kurewa kasashe kan bukatar dakile yi wa Falasdinawa kisan kare dangi a yankin na Gaza. Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Filpipo Grandi ya bukaci mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar da su kawo karshen rarrabuwar kawunan da ke tsakaninsu, don tabbatar da an tsagaita wutar da za ta dakatar da salwantar rayukan Falasdinawa a Zirin Gaza.
11/4/202320 minutes, 5 seconds
Episode Artwork

Muhimman labarun lamurran da suka wakana a cikin mako

Rundunar sojin Isra’ila ta ce dakarunta sun kai farmakin wucin gadi a arewacin yankin Zirin Gaza ta kasa a cikin daren ranar Alhamis, inda suka yi  arrangama da  mayakan Hamas a matsayin sharar fagen shirinta na kaddamar da gagarumin farmakin murkushe kungiyar ta Hamas
10/28/202320 minutes, 3 seconds
Episode Artwork

Harin asibitin Gaza ya jaanyo cece-ku-ce

 Cikin labarun da shirin makon nan ya waiwaya akwai Harin da ya kashe daruruwan mutane a babban asibitin Zirin Gaza, lamarin da fusata kasashe da dama, da hukumomi, da kungiyoyin na kasa da kasa, da sauran al’umma a sassan duniya. Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da dakile wani yunkurin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum na tserewa daga gidan da ake tsare da shi. 
10/21/202318 minutes, 26 seconds
Episode Artwork

Halin da ake ciki a Zirin Gaza bayan barkewar yaki tsakanin Isra'ila da Hamas

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' da ya saba waiwayar labarun makon da ya kare a wannan karon ya mayar da hankali kan yakin da ya barke tsakanin Isra'ila da mayakan Falasdinawa na kungiyar Hamas. Za kuma a ji yadda dubban jama’a suka gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a sassan duniya, yayin da Amurka ta jaddada goyon bayanta ga Isra’ila.
10/14/202319 minutes, 59 seconds
Episode Artwork

Mu zagaya Duniya

Masu sauraro Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin Shirin Mu Zagaya duniya daga nan sashin Hausa na Radio France International RFI………Nura Ado Suleiman zan jagoranci bitar wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata.
10/7/202318 minutes, 56 seconds
Episode Artwork

Shirin Mu Zagaya Duniya

Masu sauraro Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin Shirin Mu Zagaya duniya daga nan sashin Hausa na Radio France International RFI………Nura Ado Suleiman zan jagoranci bitar wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata. 
9/30/202319 minutes, 51 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako- 'Yan bindiga sun yi awon gaba da tarin daliban jami'ar Gusau

Shirin Mu zagaya duniya tare da Nura Ado Suleiman kamar kowanne mako ya yi bita ne kan muhimman labaran da suka faru a makon da muka yi bankwana da shi, inda a cikinsa za ku ji yadda 'yan bindiga suka sace gomman dalibai a Jami'ar tarayya ta birnin Gusau a jihar Zamfara. Haka zalika a cikin shirinza ku ji yadda Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin daukaka kara bayan matakin kotun sauraren kararrakin zabe na kwace nasarar da ya yi a zaben watan Maris.Bugu da kari shirin ya leka sauran sassan Duniya dauke da muhimman labarai na wannan mako, ciki kuwa har da dambarwar bakin haure a Italiya baya ga ziyarar Sarki Charles na 3 a Faransa baya ga ziyarar Fafaroma Francis.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
9/23/202320 minutes, 7 seconds
Episode Artwork

Mu Zagaya Duniya

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.
9/16/202320 minutes, 2 seconds
Episode Artwork

'Yan adawa sun yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' yana bitar wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata. daga cikin abbubuwan da shirin ya kawo muku, za ku ji cewa, manyan jam’iyyun adawa a Najeriya sun yi  watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin saben shugaban kasa da ta tabbatar da nasarar da shugaba Bola Tinubu da ya lashe zaben da ya gudana a karshen watan Fabarairu. da sauransu.
9/9/202319 minutes, 1 second
Episode Artwork

Bitar labaran Mako; Yunkurin ECOWAS na daukar matakan soji a Nijar

Cikin batutuwan da Shirin wannan mako ya waiwaya tare da "Nura Ado Sulaiman", akwai matakin da kungiyar Kungiyar ECOWAS ta dauka na amince wa da shirin kafa rundunar soji ta wucin gadi wadda za a yi amfani da ita wajen kai hari a kan sojojin da suka yi juyin Mulki a Nijar, idan matakan diflomasiya suka gaza haifar da ‘da mai ido. Sakamakon takunkumai da suka hada rufe iyakoki, da kuma hana hada-hadar kudade da kasashen Yammacin Afirka suka kakaba wa Jamhuriyar Nijar, yanzu haka an fara fuskantar karancin naman kaji, kifi da ake shigar da su kasar.A cikin shirin, akwai batun, mutanen da suka rasa ‘yan uwansu ko kuma suka samu raunuka a sanadiyyar harin ta’addancin da aka kai wa ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Nairobin kasar Kenya a shekarar 1998, da suka bukaci Amurka ta biya su diyya, shekaru 25 bayan faruwar wannan lamari.
8/12/202320 minutes, 15 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran Mako; Katsalandan na kasashen ketare kan Nijar zai kara dagula lamura - Rasha

Tawagar kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO ta bar Jamhuriyar Nijar a yau Juma’a, ba tare da samun ganawa da Janar Abdurahman Tchiani, shugaban mulkin sojan da suka yi juyin mulki ba, yayin da a gefe guda Rasha ta ce shiga tsakani na kasashen waje ba zai warware lamarin kasar ta Nijar ba.  Ga alama mutane da dama na bayyana rashin amincewa da matakin na soji, kuma ko su shugabannin sojin da tsohon shugaban kasa Mahaman Ousmane da wasu ‘yan Najeriay da dama, na nunarashin amincewa da haka.Amma minister harkokin wajen Senegal ta bayyana cewar muddin ECOWAS ta bada umurni, toh zasu bada sojojin su domin daukar matakin soji akan Nijar. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
8/5/202319 minutes, 26 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako; Shekarar 2023 kan iya zama shekara mafi tsananin zafi a tarihi

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kasashen yankin arewacin duniya za su ci gaba da ganin tsananin zafi sakamakon dumamar yanayi da ke ci gaba da ta’azzara, gargadin da ke zuwa a dai dai lokacin da tuni nahiyar Turai da arewacin Amurka da kuma wasu sassa a Asiya suka fara ji a jikinsu.A cikin shirin mu zagaya Duniya Rukkaya Abba Kabara ta dubi a kan wannan labari da wasu a kai.
7/22/202319 minutes, 41 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran Mako ; Sai bayan Ukraine ta fita daga yaki za ta iya shiga NATO

Biden ya shaidawa taron manema labarai a kasar Finland kwana guda bayan taron kungiyar inda mambobin kungiyar suka gaza baiwa Ukraine damar shiga NATO, "Ba batun shiga ko akasin haka bane, lokaci ake jira. Biden ya gana da shugabannin yankin Nordic a Helsinki na kasar Finland,Shugaba Niinisto ya karbi bakuncin taron da ya samu halartar firaministan Sweden, Norway, Denmark da kuma Iceland.A cikin shirin mu zagaya Duniya Rukkaya Abba Kabara ta dubi a kan wannan labari da wasu a kai.
7/15/202319 minutes, 33 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Bankin duniya ya tallafawa kasashen Tafkin Chadi da dala dubu 1

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali cikin mako mai karewa, ciki har da yadda bankin diniya ya tallafawa kasashen da ke yankin Tafkin Chadi da dala dubu daya, don murmurewa daga komabayan da suka samu sabida rikicin Boko Haram. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.....
7/8/202319 minutes, 3 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Majalisar Dinkin Duniya ta kawo karshen zaman sojojin a Mali

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali cikin mako mai karewa, ciki har da yadda Majalisar Dinkin Duniya ta kawo karshen zaman sojojinta na MUNISMA a Mali, bayan da suka kwashe tsawon shekaru 10 suna aiki. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.....
7/1/202319 minutes, 58 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Wasu attajirai 'yan yawon bude ido sun mutu a tekun Atlantic

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali cikin mako mai karewa, ciki har da yadda shugabanin wasu kasashen Afirka suka caccaki manyan kasashen duniya kan yadda suke zuba makudaden kudade a Ukraine, ba tare da duba halin da Afirka ke ciki ba, sai kuma labarin mutuwar wasu hamshakan attajirai masu yawon bude ido a kokarinsu na ziyarar sauran tarkacen jirgin ruwan Titinic.
6/24/202320 minutes, 25 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Hadarin kwalekwale ya hallaka mutane sama da 100 a Najeriya

Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitar wasu labarai da suka fi daukar hankali cikin mako mai karewa ciki harda hatsarin kwale-kwale da yayi sanadiyar mutuwar sama da mutane 100 a jihar Kwara dake Yammacin Najeriya.
6/17/202319 minutes, 54 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako - Harin Al-shebaab sansanin dakarun AU a kasar Somalia

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitan wasu labaran da suka fi daukar hankali cikin makon da muka yi bankwana da shi, masamman harin da mayakan Al-shebaab suka yi sansanin dakarun AU dake Somalia. Sai kuma korar da shugaban Rwanda Paul Kagame ya yi wa wasu manyan hafsoshinsa.
6/10/202321 minutes, 7 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Janye tallafin mai a Najeriya

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ta wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitan wasu labaran da suka wakana a makon da muka yi bankwana da shi masamman batun janye tallafin man fetur da sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tunubu ya sanar.
6/3/202320 minutes, 14 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Kungiyar kasashen Afirka ta ci ka shekaru 60 da kafuwa

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' da ke waiwayar mahimman abubuwan da suka faru a duniya a  cikin maako mai wucewa tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon, ya waiwayi bukin ciki shekaru 60 da kafuwar kungiyar kasashen Afirka, a Najeriya 'yan kasar sun bayyana abin da suke so sabuwar gwamnati mai kamawa ta yi musu.
5/27/202320 minutes, 22 seconds
Episode Artwork

Mutane 10 sun mutu a wani sabon rikici da ya barke a jihar Filato da ke Najeriya

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako kamar yadda aka saba, ya waiwayi muhimman  abubuwan da suka faru a duniya a makon da ya gabata. Daga cikin akwai halin da ake ciki a jihar Filato, inda aka akalla mutane 100 suka rasa rayukansu sakamkon wani sabon rikici da ya barke, da kuma shugabannin kasashen Afirka shida da za su yi tattaki zuwa Rasha da Ukraine, domin sulhunta yakin da kasashen suka shafe sama da shekara 1 suna gwabzawa.  
5/20/202320 minutes, 16 seconds
Episode Artwork

Rahoton MDD ya bankado kisan fararen hula da sojoji suka yi a Mali.

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya saba waiwayar mahimman abubuwan da suka faru a duniya a  cikin maako mai wucewa. Daga cikin abubuwan da shirin ya waiwaya a wannan makon, akwai rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya bayyana cewar sojojin Mali tare da dakarun kasashen ketare da ke taimaka musu a yakin da suke yi da taa'addanci sun kashe daruruwan fararen hula a shekarar 2022. Zaloka, baangarorin da ke riki da juna a Sudan sun bada dama a shigo da kayayyakin agaji inda ake da bukata.
5/13/202321 minutes, 3 seconds
Episode Artwork

Yadda bikin ranar ma'aikata ta duniya ya gudana

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako kamar yadda aka saba a kowane mako ya duba manyan abubuwan da suka wakana ne a makon da ya gabata. Shirn ya duba yadda aka gudanar da bikin ranar ma'aikata ta duniya a wasu sassan duniya, sannan ya duba batun rikicin da ya baarke a ksar Sudan, da irin kokarin da kasashen duniya ke yi na warware shi tun bayan da ya tashi a ranar 15 ga watan Afrilu a tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun kai daaukin gaggawa na musamman.
5/6/202322 minutes
Episode Artwork

Jiragen yakin sojojin Sudan sun yi ruwan bama-bamai kan dakarun RSF a Khartoum

Jiragen yakin sojojin Sudan sun yi ruwan bama-bamai kan dakarun RSF a Khartoum, duk da kara wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi da kwanaki 3. Gwamnatin Najeriya, ta soke shirin janye tallafin man fetur kafin mika ragamar mulki ga hannun sabuwar gwamnati.. Nura Ado Suleiman  a sabon shirin da ya saba waiwayar wasu daga cikin muhimman al’amuran da suka auku a makon da ya gabata, a cikin shirin ‘Mu Zagaya Duniya’ wanda ke zuwa daga sashin Hausa na RFI.
4/29/202318 minutes, 20 seconds
Episode Artwork

An fara musayar fursunoni mafi girma tsakanin Yemen da 'yan tawayen Houthi

Daga cikin labarun dashirin wannan lokaci ya tsakuro akwai taron da kasaashn Larabawa suka gudanar dominm kawo karshen matakin saniyar ware da suka mayar da Syria, sai kuma musayar fursunoni  da aka fara tsakanin gwamnatin Yemen da 'yan tawayen Houthi. A gabashin Afirka kuwa, hasarar rayuka aka samu a yayin da wasu mutane fiye da 10 suka tagayyara a Kenya saboda azumin mutuwa da ssuke yi a wani mataki na gaggawar saduwa da  Yesu Almasihu.
4/15/202318 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

'Yan bindiga sun sace mutane 100 da suka hada da mata da kananan yara a Zamfara

Sama da mata da kananan yara 100'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a dajin da ke gefen garin Wanzamai na jihar Zamfara da ke tarrayar Najeriya.Lamarin dai ya faru ne sakamakon kashe wasu 'yan ta'adda hudu da jami'an tsaron da ke baiwa garin kariya suka yi. A cikin shirin mu zagaya Duniya da kesaba waiwayar wasu daga cilkin muhiman al'amuran da suka auku tare da Nura Ado Suleiman daga nan Rfi.
4/8/202318 minutes, 32 seconds
Episode Artwork

Matsalar ta'addanci ta tilasta rufe makarantu a Burkina Faso.

Shirin 'Mu Zagaya Duniya'  ya saba waiwayar wasu daga cikin muhimman al’amuran da suka auku a makon da ya gabata ne. A wanna tasha ta Radio France Internationale yake zuwa muku.  Daga cikin labarun da shirin wannan mako ya kunsa akwai rahoton da ya bayyana cewar matsalar hare-haren ‘yan ta’adda sun tilasta rufe akalla kashi 1 bisa 4 na yawan makarantu a Burkina Faso.  A Najeriya kuma sabon gwmnan Zamfara mai  jiran  gado ya ce babu batun sulhu tsakanin gwamatinsa da ‘yan bindiga.  
3/25/202320 minutes
Episode Artwork

Boko Haram sun gwammaci mika kansu ga sojojin bayan kazamin fadan da suka gwabza da ISWAP

Mu Zagaya Duniya na wannan makon za a ji yadda daruruwan mayakan Boko Haram tare da Iyalansu suka gwammaci mika kansu ga sojojin Najeriya,biyo bayan kazamin fadan da suka gwabza da mayakan ISWAP a jihar Borno.. Nura Ado Suleiman ne zai jagorancin shirin na wannan mako.
3/12/202320 minutes
Episode Artwork

Bitar mahimman al'amuran da suka faru a makon da ya gabata

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' yana waiwaye ne a game da mahimman abubuwan da suka auku a makon daa ya gabata, kuma yana zuwa muku ne duk mako a wan a tashar. Shirin ya kawo mana labarin yadda a ranar 1 ga watan Maris ce hukumar zabe Najeriya ta ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023, da kuma yadda manyan kungiyoyin hamayya a kasar kamar su PDP da Labour suka yi watsi da sakamakon, suka kuma kai batun a gaban kotu.
3/4/202321 minutes, 52 seconds
Episode Artwork

Yan Najeriya da suka fusata sun fansama kan titunan wasu biranen kasar

A cikin shirin Mu zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman, ya zakulo wasu daga cikin muhimman batutuwan da suka auku a makon da ya gabata. A wannan shiri za a ji yadda dubun dubatar yan Najeriya suka fansama kan tituna wasun wasu birane a sassan kasar domin zanga-zanga kan karancin sabbin takardun naira da kuma dakatar da amfani da tsaffin.
2/18/202320 minutes, 11 seconds
Episode Artwork

Girgizar kasa ta kashe mutane fiye da dubu 23 a Turkiya sa Syria

Daga cikin manyan al’amuran da shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya waiwaya akwai halin da ake ciki a kasashen Turkiya da Syria, inda girgizar kasa ta kashe mutane fiye da dubu 23. Akwai kuma rahoto akan girgizar kasa mafi muni da aka gani a duniya cikin karni na 21.
2/11/202319 minutes, 48 seconds
Episode Artwork

Akalla kananan yara 49 suka mutu sakamakon nutsewa a ruwa a Pakistan

Shirin Mu zagaya Duniya na wannan mako ya mayar da hankali a kan Pakistan, in da akalla kananan yara 49 suka mutu sakamakon nutsewa a ruwa bayan kifewar Kwalekwalensu. Hatsarin ya auku ne a yayin da yawan wadanda suka mutu a harin bam din da aka kai kan Masallaci a Pakistan din ya kai mutane 100, yayin da wasu fiye da 200 suka jikkata.Nura Ado Suleiman daga sashin Hausa na RFI zan jagoranci gabatar da shirin.
2/4/202318 minutes, 38 seconds
Episode Artwork

Burkina Faso ta nanata umarnin da ta baiwa sojojin Faransa na su fice daga kasar

‘Mu Zagaya Duniya’ mai bitar wasu daga cikin muhimman labaran, da suka fi daukar hankali a makon da ya kare, Nura Ado Suleiman daga sashin Hausa na RFI zan jagoranci gabatar da shirin. daga cikin labaren za ku ji cewa Gwamnatin sojin Burkina Faso ta nanata umarnin da ta baiwa sojojin Faransa cewa su fice daga kasar.
1/28/202320 minutes, 26 seconds
Episode Artwork

Bitar Labaran Mako: Saukar farashin kayaki a Najeriya karon farko cikin watanni 11

Shirin Mu zagaya Duniya tare da Rukayya Abba Kabara ya yi duba kan muhimman labarun makon da suka gabata, inda a wannan karon ta yi duba kan satar mata fiye da 50 a Burkina Faso kana korar wasu masu sarautun gargajiya a Najeriya saboda taimakawa 'yan bindiga kana saukar farashin kayaki a Najeriya karon farko cikin watanni 11.
1/21/202319 minutes, 33 seconds
Episode Artwork

Bitar Labaran Mako- Rashin kulawar lafiya ta sa mutuwar yara miliyan 5 a 2022

Shirin Mu zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman kamar kowanne mako ya yi bita kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi, ciki har da rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ke cewa yaro guda na mutuwa a duk dakika hudu da rabi saboda rashin kulawar lafiya musamman a kasashe masu tasowa.
1/14/202319 minutes, 8 seconds
Episode Artwork

Labaran karshen mako: Yadda aka yi jana'izar Pele da Fafaroma Benedict

Shirin Mu zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman ya tabo muhimman batutuwan da suka faru a makon da muke ban kwana da shi na farko a sabuwar shekarar 2023, kuma shirin na yau ya tabo tarukan birne Pele da Fafaroma Benedict, baya ga matsin lambar da Rasha ke fuskanta sakamakon harin Ukraine da ya kashe sojojin kasar fiye da 80 sai kuma gano gawarwakin wasu fararen hula 28 a Burkina Faso.
1/7/202319 minutes, 53 seconds
Episode Artwork

Mutane akalla 890 ‘yan ta’adda suka kashe a Nijar cikin shekarar 2021

Mai sauraro Nura Ado Suleiman cikin shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako  inda za ku ji cewa a Jamhuriyar Nijar,hukumar kare hakkin dan adam ta kasar ta wallafa rahoton da ya bayyana cewar, mutane  akalla 890 ‘yan ta’adda suka kashe a kasar cikin shekarar barra ta 2021.
12/24/202218 minutes, 56 seconds
Episode Artwork

Matakin gwamnatin jamhuriyar Nijar na fara maido da tsaffin sojoji bakin aiki

Mu Zagaya Duniya, shirin da ya saba yin waiwaye ko bitar wasu daga cikin muhimman labarai dangane da lamurran da suka auku a makon da ya kare. Daga cikin batutuwan da shirin zai sake tisawa kuwa a wannan karon akwai matakin gwamnatin jamhuriyar Nijar na fara maido da tsaffin sojoji bakin aiki, domin taimaka mata wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar. Masu sauraro Nura Ado Suleiman daga sashin Hausa na Radio France International ke muku maraba cikin Mu Zagaya Duniya
12/17/202221 minutes, 27 seconds
Episode Artwork

Mu zagaya Duniya- Ziyarar Shugaba Macron a Amurka

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin ziyarar da ya kai Amurka,ya jaddada aniyar kasar sa na tafiya kafada da kafada da Amurka duk da sabani ra'ayoyi da aka samu a baya.Shugaban Amurka Joe Biden ana sa bangaren ya fada cewa ya amince da shugaban Faransa Emmanuel Macron kan daidaita hanyoyin da bangarorin biyu ke bi kan batutuwan da suka shafi yanayi da makamashi a daidai lokacin da kasashen Turai ke nuna damuwa kan kariyar Amurka. Bashir Ibrahim Idris a cikin shirin mu zagaya Duniya ya tabo wasu daga cikin muhiman batuttuwa na wannan mako.
12/3/202220 minutes, 55 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Adadin yawan al'umma ya kai biliyan takwas

Shirin Mu Zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitar muhimman labaran da suka faru a makon da muka yi ban kwana da shi, inda labarin yadda yawan jama'ar Duniya ya kai biliyan 8 ya fi jan hankali al'umma. Ayi saurare Lafiya.
11/19/202219 minutes, 50 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Faduwar darajar kudin Najeriya Naira

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya sake waiwaya yadda gobarar daji ta kone gonakin da fadinsu ya zarce kadada dubu 3,700 a Jamhuriyar Nijar,A Najeriya kuwa, darajar kudin kasar ce ta cigaba da faduwa a makon da ya kare, yayin da kuma matsalar karancin dala ta yi kamari, lamarin da ya kai ga kame gwamman ‘yan canji a manyan biranen kasar. Sai kuma India, inda jami’an tsaro suka cafke wasu mutane biyo bayan rushewar wata tsohuwar gada, lamarin da yayi sanadin mutuwar mutane fiye da 130.
11/5/202220 minutes, 13 seconds
Episode Artwork

Kasar Mali ta bukaci Faransa ta mutunta wasu ka'idoji kafin dawo da hulda tsakaninsu

Shirin mu zagaya duniya na wannan mako zai yo dubi ne a kan wasu muhiman labaren Duniya tare da Nura Ado Suleiman. A cikin shirin za ku ji halin da ake ciki dangane da tsamin dangantaka tsakanin kasar Mali da Nijar,kazzalika za ku ji a ina aka kwana dangane da wasu kasashen da suka hada da Najeriya,Nijar da yankin Turai.
10/29/202218 minutes, 44 seconds
Episode Artwork

Chadi: Zanga-zangar adawa da mulkin Soji ta yi sanadin mutuwar gwamman mutane

Shirin mu Zagaya Duniya’ mai bitar wasu daga cikin muhimman labaran, da suka fi daukar hankali a makon da ya kare, tare da Nura Ado Suleiman daga sashin Hausa na RFI A na gaf da karkare mako, Fira ministan Chadi Saleh Kebzabo ya sanar da kafa dokar takaita zirga-zirga a cikin manyan biranen kasar, bayan da aka tabbatar da mutuwar akalla mutane 50 sannan wasu sama da 100 suka jikkata, yayin zanga-zangar da dubban mutane suka yi a alhamis da ta gabata.
10/22/202220 minutes, 31 seconds
Episode Artwork

Ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar ‘yan Najeriya sama da 500

Shirin mu Zagaya Duniya’ mai bitar wasu daga cikin muhimman labaran, da suka fi daukar hankali a makon da ya kare, tare da Nura Ado Suleiman daga sashin Hausa na RFI A farkon makon da ya kare Sabuwar kididdigar da gwamnatin Najeriya ta fitar, ta nuna cewa ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar ‘yan kasar sama da 500, yayin da kuma iftila’in ya shafi wasu mutanen kusan miliyan daya da rabi a sassan kasar.
10/15/202220 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran makon da ya gabata: Mutuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth ta 2

Shirin Mu zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman bisa al'ada kan bibiyi manyan labaran da suka faru a makon da muke shirin ban kwana da shi, inda a wannan karon ya tabo manyan labarai ciki har da mutuwar sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ta 2 wadda ta shafe shekaru 70 ta na mulkin gidan sarautar Birtaniya.
9/10/202221 minutes, 11 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Yara miliyan 240 da basa zuwa makaranta a sassan Duniya

Shirin Mu zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman da ke bitar muhimman labaran da suka faru a makon da ya gabata, a wannan karon shirin ya yi waiwaye kan wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ke nuna yadda aka samu karuwar yaran da basa zuwa makaranta zuwa yara sama da miliyan 240 sai kuma yadda yara dubu 22 suka rasa rayukansu saboda gurbatar iska a jihar Lagos. Ayi saurare Lafiya. 
9/3/202220 minutes, 10 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Ambaliyar ruwa ta tagayyara mutane dubu 300 a Chadi

Shirin Mu zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman ya yi duba kan muhimman labaran da suka fi daukar hankali a makon da muke bankwana da shi ciki har da yadda mutane fiye da dubu 300 suka tagayyara a Chadi saboda tsannatar ambaliyar ruwa sai kuma ziyarar Macron a Algeria kana tsokacin masana game da rikicin Rasha da Ukraine.
8/27/202220 minutes, 1 second
Episode Artwork

Bitar labaran mako- Yadda Sojin Najeriya suka yi hobbasa a yaki da ‘yan ta’adda

A cikin shirin ‘Mu Zagaya Duniya’ mai bitar wasu daga cikin muhimman labaran, da suka fi daukar hankali a makon da ya kare sojin saman Najeriya sun halaka ‘yan ta’adda da dama yayin hare-haren da suka kaddamar kansu a jihohin Kaduna da Neja, sai Afghanistan, inda kungiyar Taliban ta cika shekara guda cif da sake kwace iko da mulkin kasar, bayan shafe shekaru 20 tana gwabza yaki da dakarun Amurka.
8/20/202218 minutes, 51 seconds
Episode Artwork

Mu zagaya Duniya-‘Yan bindiga sun kai hari tare da fasa gidan Yari a Jamhuriyar Dr Congo

Cikin shirin ‘Mu Zagaya Duniya’ mai bitar wasu daga cikin muhimman labaran, da suka fi daukar hankali a makon da ya kare, Nura Ado Suleiman daga sashin Hausa na RFI zai jagoranci gabatar da shirin na wannan lokaci. A cikin  shirin za ku ji cewa shalkwatar Tsaron Najeriya ta ce ‘yan ta’adda fiye da dubu 1 da 700 sun mika wuya, yayin da sojoji suka kashe wasu da dama cikin makwanni biyu. 
8/13/202220 minutes, 13 seconds